Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Babu wata mafita ta soji ga duk wani lamari da ya shafi Iran. Iraniyawa ba za su taɓa sunkuyar da kai ba ga duk wani matsin lamba ko barazana.
Iran tana son dukkan ƙasashe mambobin BRICS da duk wani wanda ke da alhakin da ke cikin al'ummar duniya da su fito karara su yi Allah wadai da take hakkin ƙasa da ƙasa da Amurka da Isra'ila ke yi, gami da harin da suka kai wa Iran ba bisa ka'ida ba; su kuma hana siyasanyar da hukumomin ƙasa da ƙasa.
Sayyid Abbas Araghchi: Mashigar Hormuz a yanzu tana fama da harin Amurka da kawanyar da suka dora mata fiye da kowane abu.
A ganinmu, mashigar Hormuz a buɗe take ga dukkan jiragen ruwa na kasuwanci, amma dole ne su ba da hadin kai ga sojojin ruwanmu.
Ba mu haifar da wani cikas ba; Amurka ce ta sanya killacewar, kuma ina fata wannan yanayin zai ƙare tare da kawar da wannan kawanyar da ta saba wa doka da Amurka ta dora.
Martanin Araghchi Ga Iƙirarin UAE: Haɗin Kai Da Isra'ila Ma Bai Ba Ku Kariya Ba.
Ministan Harkokin Wajen Iran: Haɗin kai da ku da Isra'ilawa ma bai ba ku kariya ba, ku sake duba manufofinku game da Iran.
Ban ambaci sunan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a cikin jawabina ba, don kiyaye hadin kai, kuma na gwammace ma ban yi nuni garesa ba. Amma a gaskiya dole in ce UAE ta kasance da hannu kai tsaye a cikin ayyukan ta'addanci a kan ƙasata. Lokacin da wannan hari ya fara, sun ƙi ko yin Allah wadai da shi.
Sun ƙyale a yi amfani da ƙasarsu wajen harba manyan bindigogi da kayan aiki a kanmu.
Kuma jiya ne aka bayyana cewa Netanyahu a lokacin yaƙin ya ziyarci UAE da Abu Dhabi. Hakan kuma ya bayyana cewa suna da hannu a wadannan hare-haren, watakila ma sun kai hari kai tsaye a kanmu. Don haka UAE abokiyar tarayya ce a wannan hari kuma babu shakka a kan hakan.
Ga duk wanda ya halarci taron, abin mamaki ne cewa wakilin UAE bashi da wata matsala sai dai maganar yaƙi da martanin da Iran ta mayar wa Amurka a cikin ƙasarsu. Wannan lamari abin takaici ne matuka, sai na zama dole na bayyana wa membobin taron da ƙasashen da ke BRICS dalla-dalla cewa mu ba ma yawan tada waɗannan batutuwa, amma duk da haka kowane abu yana da iyaka.
UAE ta tsaya tare da Amurka da Isra'ila a wannan yaƙi. Na ce ba ma so mu shiga waɗannan batutuwa ne don kiyaye haɗin kai da daidaiton BRICS, amma tunda wakilin UAE ya tada batun, sai da muka fayyace gaskiya ga al'ummar duniya.
A ƙarshe kuma na ba wa wakilin UAE shawara cewa sahayoniyar Isra'ila da Amurka ba za su iya kawo musu tsaro ba.
..........
Your Comment